Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), sun kama wasu mata biyu da ake zargi da kai wa ‘yan bindiga makamai da alburusai a Kaduna, Neja da kewaye.
An kama wadanda ake zargin Rashida Umar da Rukaiya ladan ne a Fadan-Karshe, karamar hukumar Sanga a Kudancin Kaduna.
Rahotanni sun tattaro cewa, jami’an DSS sun damke matan biyu da ake zargin suna kai alburusai ga ‘yan bindiga a garin Kontagora na jihar Neja.
Majiyar tsaro ta bayyana cewa, an kama wadanda ake zargin dauke da harsashi na AK-47 guda 1,000.
Kame mutanen biyu na zuwa ne kwana biyar bayan da dakarun Operation Safe Haven (OPSH) suka gano wata masana’antar kera bindigogi a Kafanchan, karamar hukumar Jema’a a Kudancin Kaduna.
An gano wannan lamarin ya biyo bayan wani samamen da jami’an leken asiri suka yi na tsawon mako guda, wanda a karshe ya kai ga cafke wani dan bindiga da ake nema ruwa a jallo, Napoleon John, wanda ke cikin jerin sunayen ‘Operation Safe Haven’ da ake nema ruwa a jallo. Allah yakawo karshen abun.