Ma'aikatar kirkire-kirkire ta kimiya da fasaha ta tarayya sashen kiwon lafiya da aikin likitanci tare da hadin gwiwar ma'aikatar jin dadin jama'a da ci gaban al'umma ta jihar kaduna sun shirya taron horaswa na yini daya kan yadda ake amfani da fasaha don rage nauyin mata.
Kwamishiniyar ma’aikatar kula da jin dadin jama’a da ci gaban jama’a Hajiya Rabi Salisu ta ce manufar horaswar ita ce karfafawa mata don rage halin da mutane ke ciki a halin yanzu saboda iskar gas da itacen wuta na da tsada saboda cire tallafin.
Daya daga cikin mahalarta taron daga ma’aikatar kirkire-kirkire ta gwamnatin tarayya Mrs.Oluwatoyin jegede ta ce shirin na rage radadin aikin mata musamman matan karkara da ke fama da su ta hanyar ba su murhun girki da kuma koya musu yadda ake yin bulo da za a iya amfani da su a matsayin mai.
An horas da mata daga kananan hukumomi daban-daban a fadin jihar kan yadda za su rika amfani da murhun gida wajen girkinsu, bayan horar da matan an baiwa kowace mace murhun gida da kuma kudin sufuri.
Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun yabawa gwamnati tun daga tarayya har zuwa jiha bisa tallafin da suka ba su a daidai lokacin da suke cikin bukata sannan kuma suna godiya ga kwamishinan da ya ba su irin wannan dama.