Malam Tahir Umar ya baiyana Mahimmancin SALLAH, Sirrorin da Mahimmancin fadar Ameen.


A jiya ne juma'ah 14 ga watan Rabi'ul Awwal dai dai da 29 ga September 2023, Babban limamin masallacin juma'ah Malam Tahir Umar yayi Kira ga daukacin Al'ummar musulmai da suyi riko da SALLAH domin samun kusanci da Allah madaukakin Sarki. Ya Kara da cewa SALLAH na daya da abinda Allah yake so da bawansa yayi riko da ita. SALLAH nasa bawa ya dinga Tina ubangijinsa a ko Wana lokaci domin ibada ce da bawa zai yi sau biyar ako wacce Rana inda yayi nuni da sallolin guda inda yace sallar Assubah SALLAH ce mai sa bawa ya fara gadar da ubangijinsa bayan ya tashi daga bacci sanan sallar Isha'i ita kuma SALLAH ce Mai sa bawan Allah yayi bankwana da Allah bayan Allah yabashi ikon gannin wuni lafiya kuma gashi ya fuskanci dare. 

Sannan yayi Kira ga Al'umma da su dinga fadin Ameen da kyau yayin da liman yakai karshen suratul fatiha a lokacin SALLAH. Domin fadin Ameen koyi ne da Annabi Muhammad S.A.W. 

 Yayin da yake baiyana sirin SALLAH, yace SALLAH nasa baya ya Kara Jin tsoron Allah, Yana sa bawa ya dinga Tina ubangijinsa akai akai, tana sa bawa yasamu kwanciyar hankali a rayuwar sa, tana sa bawa yasamu biyan bukatun sa.

A karshe yayi Kira da Al'umma su dinga rokon Allah ya biya masu bukatun su yayin da suje sujjada a gurin SALLAH 

Post a Comment

Previous Post Next Post