Gwamnan a lokacin da yake aza harsashin ginin babbar makarantar sakandare a Nasarawan Rigachikun, karamar hukumar Igabi, ya ce kafa ginin na nuni da cewa an fara gina makarantu 62 a fadin jihar.
Ya ce manufar gina makarantun shi ne a tabbatar da cewa kowane yaro ya je makaranta.
Sanata Uba Sani ya bayyana cewa, a karkashin shirin sabunta kayayyakin more rayuwa na makarantun, za a gina ajujuwa, dakunan gwaje-gwaje, guraben gudanar da mulki, dakunan hada-hadar kudi, da bandakuna.
A cewarsa, saboda yawan kudaden da gwamnatinsa ke baiwa ilimi gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko a wannan fanni.
Ya kuma ba da tabbacin sa ido sosai kan yadda ake gina makarantun tare da tabbatar da cewa, an samar da ingantattun ayyuka.
Sanata Uba Sani ya nanata cewa, a Kaduna karatun Firamare da Sakandare kyauta ne.
Hakazalika Gwamna Uba Sani ya kaddamar da aikin gina hanyar karkara mai tsawon kilomita 25 daga Rigachikun – Tami – Birnin Yero a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
Sanata Uba Sani ya ce hanyar idan aka kammala za ta saukaka jigilar kayayyakin amfanin gona daga yankunan karkara zuwa yankunan Birane.
A cewarsa, nan da ‘yan kwanaki masu zuwa, zai kaddamar da aikin gina wasu hanyoyi guda 31 a cikin yankunan karkara na dukkanin kananan hukumomin.
Gwamnan ya samu rakiyar mataimakiyarsa Dr Hadiza Sabuwa Balarabe da kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna Yusuf Dahiru Liman da kwamishinan ilimi Farfesa Sani Bello da sauran jami'an gwamnati.