Uba Sani ya yi bikin kaddamar da aikin gina titin Anchau - Gadas - Palla mai tsawon kilomita ashirin da biyu a karamar hukumar Kubau da Ikara.


 Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi bikin kaddamar da aikin gina titin Anchau - Gadas - Palla mai tsawon kilomita ashirin da biyu a karamar hukumar Kubau da Ikara.

 Da yake jawabi yayin taron, Gwamnan ya ce titin na daya daga cikin hanyoyin karkara talatin da biyu da gwamnatinsa ta bayar, a wani bangare na shirin raya karkara.

 Gwamnan ya kara da cewa, hanyar tana da mahimmaci domin ba wai kawai zai saukaka zirga-zirgar jama’a ba, har ma da inganta safarar kayan amfanin gona daga gonaki zuwa kasuwanni, ta yadda za a bunkasa karkara da tattalin arzikin cikin gida.

 Tun da farko a jawabin maraba shugaban karamar hukumar Kubau, Alhaji Musa Sale Banki ya yabawa gwamnan bisa cika daya daga cikin alkawuran yakin neman zabe da ya yi a lokacin yakin neman zabe.

Post a Comment

Previous Post Next Post